An tarwatsa 'yan Biafra a Port Harcourt
November 10, 2015'Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi amfani da harsasan roba da kuma hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa zanga-zangar da masu rajin kafa kasar Biafra suka gudanar a birnin Port Harcourt da ke yankin Kudu maso gabashin Najeriya. Suna nema a sako wani dan aware mai suna Nnamdi Kanu da aka kame tun watan Kktoba sakamakon watsa shirye-shiryen a wata rediyo da suka kafa ba bisa ka'ida ba.
Wasu da suka shaidar da gangami na Biaffra sun bayyana cewar jirage masu saukar angulu sun yi shawaki a sararin samaniyar birnin Port harcourt. sai da kuma kwamishinan 'yan sandan wannan jiha ta Rivers ya karyata rade-raden da ake yayatawa cewa sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa 'ya awaren na Biafra.
Irin wannan yunkuri na neman ballewa daga Najeriya ya taba haddasa yakin basasa a baya, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane miliyan daya.