An tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Abidjan na Kodivuwa | Labarai | DW | 30.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Abidjan na Kodivuwa

Dakarun tsaron Ivory Coast wato Kodivuwa sun yi harbi cikin iska tare da harba hayaki mai sa hawaye don tarwatsa masu zanga-zanga dake macin zuwa fadar shugaban kasa Laurent Gbagbo a yau lahadi, ranar da ya kamata a gudanar da zabe a cikin kasar. Masu zanga-zangar dai na adawa ne da kara wa´adin shugabancin Gbagbo. Wakilin kamfanin dillancin labarun AFP ya ce wasu ´yan adawa 400 da suka shiga cikin jerin gwano sun samu danganawa ga fadar shugaban. Macin dai na daga cikin jerin zanga-zangar da aka gudanar a fadin kasar baki daya abin da ya sanya fargaba game da makomar siyasar kasar dake yammacin Afirka. A birnin Abidjan matasa kimanin dubu 4 ne suka halarci taron gangamin da aka yi a filin wasanni na dake unguwar Trechville, yayin da a Buake cibiyar ´yan tawaye fiye da mutane dubu 10 suka shiga cikin zanga-zangar neman shugaba Gbagbo ya sauka daga kan karagar mulki bayan cikar wa´adin shugabancin sa da karfe 12 daren yau lahadi.