An tantana tsakanin F W Steinmeir da Ali Larijani a game da rikicin nuklea | Labarai | DW | 05.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tantana tsakanin F W Steinmeir da Ali Larijani a game da rikicin nuklea

Ministan harakokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeir, ya gana da shugaban tawagar Iran , a tantanawar rikicin makaman nuklea Ali Larjani.

Tawagogin ƙasashen 2, sun yi bitar halin da ake ciki a game da wannan badaƙala.

Kakakin ministan harakokin wajen Jamus, ya bayyana gamsuwa da tantanawar, duk da cewar ba ta cimma wani sakamakon azo a gani ba.

Ranar alhamis da ta wuce, a ka koma tebrin shawara, tsakanin Iran da ƙungiyar gamayya turai, a game da wannan rikici.

Har yanzu hukumomin Teheran, sun yi tsayuwar gwamen jaki,a game da aniyar su, ta bunƙasa makashin nuklea.