An tallafawa Bangladesh da Dola miliyan 250 | Labarai | DW | 22.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tallafawa Bangladesh da Dola miliyan 250

Wakilan ƙasashen Duniya a birnin Dhaka sun yi alƙawarin bawa Bangladesh Dola miliyan 200, a matsayin tallafi. Ƙuɗaden a cewar wakilan za a tallafawa waɗanda bala´in guguwar Sidr ta afkawa ne. Guguwar ta Sidr dake ɗauke da ruwan sama, a yanzu haka ta yi ajalin mutane sama da dubu uku. Har ila yau guguwar ta Sidr ta kuma yi sanadiyyar lalata gidajen kwanan wasu sama da dubu biyu. Yankin kudu maso yammacin ƙasar ne a cewar rahotanni ya fi fuskantar ta´annatin guguwar ta Sidr.A yanzu haka dai Jami´an bayar da agajin gaggawa na ci gaba da aikin ceto na jigilar abinci da magunguna izuwa wannan yanki.