An tafi Charles Taylor zuwa Saliyo | Labarai | DW | 29.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tafi Charles Taylor zuwa Saliyo

Tsohon shugaban kasar liberia charles Taylor ya isa kasar sa a yau laraba,inda dakarun Majalisar Dinkin Duniya suke dakonsa a filin jirgin saman birnin Monrovia inda ya sauka.

Kanfanin dillancin labarai na Reuters ya bada rahoton cewa,Jamian Majalisar Dinkin Duniya dauke da makamai suka wuce da taylor cikin wani jirgi mai saukar angulu na majalisar zuwa saliyo.