An tabbatar da sakin ´yar Birtaniya da aka yi garkuwa da ita a Zirin Gaza | Labarai | DW | 31.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tabbatar da sakin ´yar Birtaniya da aka yi garkuwa da ita a Zirin Gaza

Wata kungiyar ´yan takifen Falasdinawa dake kiran kanta kungiyar Baradan Mujahideen ta Birnin Kudus ta ce ita ta yi garkuwa da wata ma´aikaciyar agaji ´yar Birtaniya da iyayen ta. A jiya da daddare kungiyar wadda kawo yanzu ba´a san ta ba, ta saki turawan 3 a Zirin Gaza. A ranar laraba ´ya´yan kungiyar suka sace mutanen a garin Rafah. Ko da yake ba´a san yadda aka yi aka sake su ba, amma kungiyar ta ce ta sako su a wani mataki na fatan alheri. Masu garkuwan sun ce manufar su ita ce su jawo hankalin Birtaniya da kuma KTT su matsawa Isra´ila lamba ta biya wasu bukatu da dama ciki har da sakin firsinoni sannan ta janye dakarun ta daga Gabar Yammacin Kogin Jordan.