1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tabbatar da mutuwar wata Bajamushiya a ta'asar Abidjan

Mohammad Nasiru AwalMarch 14, 2016

Daraktar cibiyar yada al'adun Jamus ta Goethe Institut na daga cikin wadanda suka mutu a hare-haren ta'addancin birnin Abidjan.

https://p.dw.com/p/1ICqr
Elfenbeinküste Anschlag Grand Bassam in Abidjan
Alassane Ouattara a gaban daya daga cikin otel-otel da aka kai wa hariHoto: Reuters/L. Gnago

Wata Bajamushiya na daga cikin mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren ta'addancin da aka kai kan wasu otel-otel guda uku a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire a ranar Lahadi, kamar yadda ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi bayani. A halin da ake ciki cibiyar yada al'adun Jamus ta Goethe Institut ta tabbatar da bayanan da tashar DW ta bayar cewa, daraktar cibiyar Henrike Grohs na daga cikin wadanda aka kashen. Tun shekaru biyu ke nan Grohs ke jagorantar cibiyar. Akalla mutane 22 suka rasu a hare-haren. Shugaba Alassane Ouattara ya ce 'yan sandan kasar sun kashe maharan su shida, inda ya kara da cewa:

"Kasar Cote d'Ivoire ba za ta taba lamunta da hare-haren ta'addanci ba. Godiya ta tabbata ga dakarun tsaronmu wadanda cikin sa'o'i uku zuwa hudu suka kawo karshen hare-haren kuma suka shawo kan lamari. Ina gode wa sojojinmu."

Kungiyar Al-Kaida reshen arewacin Afirka ta dauki alhakin kai hare-haren.