1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An taba samun shugaban kasa da ya rike Ministan man fetur?

Abdullahi AliyuOctober 23, 2015

Akwai wasu lokuta da ake samun shugaban kasa da ya rike mukamin Ministan wani bangare saboda kundin tsarin mulki kan amince da haka.

https://p.dw.com/p/1GtNm
Nigeria Symbolbild Muhammadu Buhari Anti-Korruptions-Offensive
Hoto: picture-alliance/AP Photo/C. Owen

A Najeriya an taba samun shugaban kasar da ya rike Ministan man fetur, bayan ya nada karamin Minista a wannan ma'aikata ta albarkatun man fetur, wato a zamanin mulkin shugaba Obasanjo a karo na biyu, da ya dawo a matsayin shugaban kasa karkashin mulkin farar hula na dimokaradiyya a shekarar 1999 zuwa 2007. Ya kuma rike Ministan sufuri a wannan zamani na kankanin lokaci, kafin ya nada marigayi Bola Ige a matsayin babban Ministan ma'aikatar. Kuma dai kowace kasa a Afirka tana da irin tsare-tsarenta da ya sha banban da kowace kasa, kowace kasa tana da yadda take tafiyar da tsarin mulkinta kamar yadda aka tanadar mata.

Nigeria National Petroleum Corporation Öl-Industrie Korruption
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya bada damar shugaban kasa ya nada Ministoci, wannan wajibi ne, domin ba zai yiwu ayi gwamnati babu Ministoci ba. Haka idan kaje ga jihohi tsarin mulki ya bada damar a nada Kwamishinoni, amma tsarin mulki bai ce lallai sai an nada Minista a kowane bangare ba, dan haka ba lallai bane sai shugaban kasa ya nada Ministan fetur, Ministan kudi, Ministan noma da sauransu ba. Wato kowace ma'aikata za a iya rage fadinta ko a kara fadinta.

Kuma shugaban kasa yana da 'yancin ya nada Minista a duk inda yaga dama kuma yana da damar ya rage yawansu ko ya kara yawansu. Inda kuma baya son ya tura Minista ya zamanto shine yake son ya duba bangaren, to yana da ikon ya duba wurin saboda ai shi, a tsarin mulkin Najeria shugaba ne mai cikakken iko.

Unabhängigkeitstag in Nigeria 2015
Hoto: DW/U. Musa

Saboda haka dole ne dai a nada Ministoci a kasa, amma idan ya rike Ministan wani bangare ba laifi bane a kundin tsarin mulkin Najeriya.