1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Polen Tragödie

April 12, 2010

Hukumomi a ƙasar Poland sun ware mako guda na yin zaman makoki da aka soma yau

https://p.dw.com/p/MtmG
Mutane na ajiye furani a wani dandali a Warso domin tunawa da waɗanda suka mutuHoto: AP

An soma zaman makoki na mako  guda a yau a ƙasar Poland dangane da rashin da aka samu na shugaba Lech Kaczyski da mai ɗakinsa dakuma  wasu mayan jami'an gwamnati 95, a haɗarin jirgin saman da suka yi a yammacin ƙasar Rasha a ranar Asabar da ta wuce  suna kan hanyarsu ta  halartar wani biki a Katyn domin tunawa da kisan kiyasu da yan sanda leƙen asiri na tsohuwar Tarayya Soviet suka yi  akan wasu duban ´yan Poland din.

A tsawon mako guda na zaman makokin, an tsaida wasu harakoki na kasuwanci dakuma bukukuwan da aka shirya gudanarwa, sannan  ƙasar Rasha ma ta ware ranar yau saboda zaman makokin .

Wani jami'in gwamnatin ya ce za a gabatar da gawar mamanci ga jama´a a gobe talata a fadar shugaban ƙasar dake Warso kokuma Varsovie.

Yau kuma aka shirya wakilai na fadar shugaban ƙasar zasu gana da na ofisin Fraministan  domin tsara jana´iza mariganyi Kacznski wanda har yazuwa yanzu ba a saka rana ba ko kuma gurin da za a yi jana´izar

Wannan haɗari da ya faru ya kiɗimar da al´umar ƙasar Polond waɗanda har yanzu suke cikin alhini dakuma jimami dangane da wani rashi da aka yi da jama´a suke ciki da hawaye

Wani mutun da ke cikin jama´ar da suke zaman makokin ya bayyana abin da cewa wata sarauta ce ta Allah

Wannan wani abu ne na al´ajabi dama bamu san inda za mu sa kanmu ba,kuma ni zai zame a gareni abin bayar da labari zuwa gaba ga ´ya´yana.

Ko ina a cikin birinai na ƙasar ta Polond da ma sauran ƙasahen waje ana ta gudanar da adduoi'I a cikin majami'u da kuma ajiye furannni domin tunawa da mutane da suka mutu

Waɗanda kusan al´uma ƙasar ke kallon wani lamari na daban na ƙara samun mutuwar ƙurraru da maillimanta na ƙasar ta Polod a cikin wannan haɗari, bayan kisan ƙare dangin da hukumomin tsohuwa Tarayyar Soviet suka ƙaddamar akan yan ƙasar kimani 22000 soja da kwararu shekaru 70 da suka wuce a katyn.

Abinda a yanzu ake tunanin cewa ranakun tuni sun zama biyu na shekara ta 1940 dakuma shekara ta 2010

Komorowski shine shugaban Majalisar ɗokoki na ƙasar, yace

 babban rashine aka samu a duniya na mutuwar wannan jigo abune da ya zomana to amma babu yadda za mu yi amma mu dukannin mu yan ƙasar Poland sai mu rungumi ƙadara mu kuma maida hankali tare domin tunani gaba cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

A halin da ake ciki dai ,gaytumar Lech Kaczynski wace ta ke fama da rashin lafiya cikin halin mutu kokawai rai kokwai na kwance a asibiti ana jiyarta sanan haryan zu ba a shedamata cewa ɗanta ya rasu saboda halin da ta ke ciki ,kuma ma iyalan ba sa fatan a sanar da ita.

Sanan yanzu haka hukumar leƙen asiri ta KGB ta Rasha da jami'ai na ƙasar Poland na cikin gudanar da bincike domin gano dalilan da ya sa matuƙin jirgin saman ya ƙi ya bi umarnin maikata filin saukar jiragen smolens har so ukku cewa kada ya sauka sabo a kwai hazo,

masu lura da al amura na cewa watakila umarni ya samu daga shugabannin dake gaugawa zuwa halarta bikin na katyn ,to amma a yanzu sai dai a jira abinda bincikken ya tabatar.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita       : Yahuza Sadissu Madobi