1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soma rajistar masu zabe a Cote d'Ivoire

Gazali Abdou Tasawa
June 18, 2018

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Cote d'Ivoire ta soma aikin rajistar masu zabe a shirye-shiryen zabukan 2020

https://p.dw.com/p/2zo7T
Elfenbeinküste Präsidentschaftswahl Alassane Ouattara
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

A kasar Cote d'Ivoire hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta soma a wannan Litinin aikin rajistar masu zabe a shirye-shiryen zabukan 2020 da suka hada da na shugaban kasa. Hukumar zaben ta ce akwai mutane kimanin miliyan uku da suka kai shekarun yin zabe amma ba sa a cikin girgam din zaben kasar na yanzu mai kunshe da mutane miliya shida da dubu 300 a kasar da ke da yawan al'umma da ya kai miliyan 25. 

Za a dai share tsawon mako daya ana gudanar da aikin rajistar masu zaben a wurare sama da 10,000 da aka tanada. Sai dai kawancen 'yan adawar kasar wanda ya kunshi jam'iyyun siyasa da na 'yan farar hula ya yi kira ga magoya bayansa da su kaurace wa aikin rajistar yana mai zargin cewa hukumar zaben ta kunshi kusan 'yan bangaren masu mulki ne kawai. 

Sai dai hatta jam'iyyar PDCI da ke kawancen mulki da jam'iyyar RDR ta Shugaba Alassane Ouattara ta bayyana bukatar ganin an sake yi wa hukumar zaben tsari kafin zuwa zaben na 2020.