An soki shirin Blair na gina sabbin tashoshin makamashin nukiliya | Labarai | DW | 17.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An soki shirin Blair na gina sabbin tashoshin makamashin nukiliya

Masu fafatukar kare kewayen dan Adam sun fusata dangane da wani shiri da FM Birtaniya Tony Blair ke yi da nufin kafa sababbin tashoshin makamashin nukiliya a cikin kasar. A wani jawabi da yayi wa manyan ´yan kasuwa a birnin London FM Blair ya ce yanzu an sake shiga yayin kafa tashoshin nukiliya saboda matsalar dumamar yanayi da kuma yawan dogaro akan makamashi daga ketare. Masu fafatukar kare muhalli sun yi fushi ga furucin na Blair da cewa Birtaniya zata cimma bukatunta na makamashi tare da rage fid da hayaki mai dumama doron kasa, ba tare da ta gina sabbin tashoshin nukiliya ba.