An soki lamirin kafofin yada labarun Rasha
June 5, 2006Talla
A taron ta na shekara shekara dake gudana a birnin Mosko, kungiyar buga jaridu ta kasa da kasa ta yi kakkausar suka ga kafofin yada labarun kasar Rasha. A jawabin bude taron wanda aka yi a gaban shugaba Vladimir Putin, kungiyar ta yi korafin cewa gwamnatin Rasha na kara dora hannunta a aikin watsa labaru na cikin kasar. Kungiyar ta ce hukumomi a birnin Mosko na yada wani yanayi na rashin sanin tabbas tare da matsawa ´yan jarida tace labaru da kansu. Shugaba Putin yayi watsi da wannan zargi da cewa bai da tushe bare makama.