1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An soki Amurka game da take hakkokin bil adama

Ibrahim SaniNovember 18, 2005

Masu fafutikar kare hakkin bil adama sun yi watsi da tayin da Amurka ta gabatar na kai ziyara izuwa gidan yarin Guantanamo Bay dake kasar Cuba.

https://p.dw.com/p/Bu47
Hoto: AP

To ya zuwa yanzu dai rahotanni sun shaidar da cewa wadan nan jamiai sun dauki wannan mataki ne a dalilin wasu sharudda da mahukuntan na Amurka suka ginya musu a lokacin da zasu kai wannan ziyara izuwa Gidan yarin na Guantanamo Bay, don duba irin halin da mutanen da ake tsare dasu suke ciki.

A cewar jamian kare hakkin bil adaman, daga cikin wadan nan sharudda akwai yarda da cewa ba zasu tattauna da dukkannin mutanen da ake tsare dasu a cikin gidan yarin na Guantanamo Bay ba, sai dai wasu daga cikin su.

Su kuma a nasu bangaren suka ce suna sone su tattauna da dukkannin wadan da ake tsare dasun a hannu daya kuma da jamian dake kula dasu.

A cewar wadan nan jamiai yana daga cikin tsarin aiyukan su na tattaunawa da wadanda ake tsare dasu keke da keke, ba wai kawai sun zartar da hakan bane a wannan lokaci. To amma a waje daya kuma mahukuntan na Amurka sun shaidar da cewa jamiai da suka fito daga hukumomi na bayar da agajin gaggawa ne irin su Red Cross, ake bawa irin wannan dama ta tattaunawa da wadanda ake tsare dasun ido da ido.

Daga dai cikin jamiai guda biyar da aka zaba don kai wannan ziyara izuwa gidan yarin na Guantanamo Bay,mutum uku kawai mahukuntan na Amurka suka yarjewa zuwa gidan yarin.

Daga cikin wadanda kasar ta Amurka ta yarjewa kuwa akwai,Manfred Nowak daga kasar Austria,wanda kwararre ne a iya gane halin da dan adam ke ciki ,wala, Allah ana gasa masa aya a hannu ko kuma aa, sannan akwai Asma Jahangir, dan kasar Pakistan, wanda masani ne a fannin sanin yancin dan adam a bangarori na adinai daban daban,kana na karshe, wato Leila Zerrougui, dan kasar Algeria,masani ne a fannin bawa fursuna hakkin daya dace a lokacin yana tsare.

Daga cikin wadanda aka hana kuwa akwai, Leandro Despouy dan kasar Agentina,wanda kwararre ne a fannin sanin yancin Alkalanci da kuma wakiltar wanda ake tuhuma,san nan kuma akwai Paul Hunt dan kasar New Zealand, wanda shi kuma masani ne a fannin kiwon lafiya na dan adam dake fili da kuma abin da ya shafi kwakwalwa.

A can baya dai da yawa daga cikin jamiai masu fafutikar kare hakkokin bil adama sun sha sukar gwamnatin ta Amurka bisa take hakkokin bil adama da ake yi a gidan yarin na Guantanamo Bay, wanda mallakar kasar ta Amurka ce.

A cewar ire iren wadan nan jamiai,Amurka na ajiye mutane a gidan yarin ba tare da an gabatar dasu a gaban kuliya ba, sannan kuma kaidojin da gidan yarin yake dasu a cewar jamian ya sabawa kaidojin kare hakkin fursuna.

Ba a da bayan haka, jamian sun kuma shaidar da cewa da yawa daga cikin wadanda ake tsare dasun na dandana kunar su, bayan cin mutunci da suke fuskanta daga hannun jamian tsaron dake tsare dasu.

Game da wadannan zarge zarge kuwa tuni mahukuntan na Amurka suka karya ta su da cewa,suna iya bakin kokarin su wajen ganin an kare hakkokin wadanda ake tsare dasu a gidan yarin.

Gidan yarin na Guantanamo Bay, wanda aka bude shi a shekara ta 2002, watanni kadan bayan harin sha daya ga watan satumba, a yanzu haka an kiyasta cewa akwai mutane sama da dari biyar dake cikin sa wadanda suka fito daga kasashe daban daban bisa zargi da ake musu masu sabani da juna.

A waje daya kuwa hukumar kare hakkin bil adama ta Amnesty kira ta daukaka ga kungiyyar tarayyar Turai data gaggauta gudanar da bincike ga guraren da Amurka ke ajiyar mutanen da take tuhuma da aikata laifuka,wadanda ke cikin kasashen su don sanin irin halin da suke ciki. A cewar hukumar ta Amnesty ire iren wadannan gurare na taimakawa wajen kara hauhawar aiyuka na ta´addanci a duniya.

A don haka a cewar hukumar ta Amnesty akwai bukatar daukar matakan gaggawa na sanin abin da yaka mata ayi ga ire iren gurare irin su Guantanamo Bay tun kafin lokaci ya kure, ko kuma ayi dana sani a nan gaba.