An soke tashin jirage saboda dusar kankara a Rasha | Labarai | DW | 11.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An soke tashin jirage saboda dusar kankara a Rasha

Saukar dusar kankara mai yawan gaske ta haddasa soke tsashi jiragen sama fiye da 60 daga filin jirgin sama Moscow babban birnin kasar Rasha.

Filin jiragen sama na Cheremetievo da ke arewa maso yammacin birnin na Moscow, an soke tashin jiragen sama 6, yayin da wasu jiragen 19 suka yi lattin tashi a wannan filin jirage, yayin da a birnin Domodedovo da ke kudancin birnin Moscow aka soke tashin jirgi daya sannan wasu jiragen 33 suka yi lattin tashi saboda zubar dusar kankarar da kuma gurbacewar yanayi.

Ma'aikatar yanayin kasar ta Rasha ta sanar cewa, da akwai yuyuwar karuwar saukar dusar kankarar a ranar Asabar, yayin daga na shi bangare magajin garin birnin Moscow ya yi kira ga mutanen birnin da su zauna a gidajensu har sai fitar ta zama tilas.