An shiga rana ta biyu na taron kare muhalli a Canada | Labarai | DW | 29.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An shiga rana ta biyu na taron kare muhalli a Canada

Masana ilimin kimiyya na kasa da kasa sun sanar da cewa da alama shekara ta 2005 zata kasance shekarar da akafi fuskantar yawan dumamar yanayi.

Hakan a cewar masana ilimin kimiyyar ya samo asali ne a sakamakon yawan hayaki mai dauke da iskar Carbon dioxide da ake samarwa.

Wannan dai sabuwar sanarwa tazo ne a dai dai lokacin da masanan suka shiga rana ta biyu aci gaba da tattaunawa , a game da gurbatar yanayi da kuma muhalli a duniya.

Taron na kasa da kasa ya kasance na farko irin sa a tun lokacin da aka cimma yarjejeniyar nan ta birnin Kyoto, dake muradin daukar matakan inganta yanayi da kuma muhalli.

Bayanai dai sun shaidar da cewa wakilai a kalla dubu goma ne daga kasashe 180 na kasashe daban daban na duniya ne ke halartar wannan taro.