An shiga mawuyacin halin siyasa a yankunan Falasdinawa | Labarai | DW | 17.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An shiga mawuyacin halin siyasa a yankunan Falasdinawa

Yanayin siyasa ya kara rincabewa a yankunan Falasdinawa bayan kiran da shugaba Mahmud Abbas ya yi na a gudanar da zabe na gaba da wa´adi. Wannan matakin ya janyo fargabar cewa fito na fiton da ake yi tsakanin kungiyar Hamas wadda ta lashe zaben ´yan majalisar dokoki a farkon wannan shekara da kungiyar Fatah ka iya haddasa wani yakin basasa. An kashe wani mai gadin fadar shugaban kasa sannan aka yiwa mutane da dama rauni a wani lamari da jami´an tsaro suka bayyana shi da cewa wani yunkuri ne da ´ya´yan Hamas ke yi na farma sansanin horas da masu gadin shugaban kasa. A jiya daddare an harbe wani yaro har lahira sannan akalla mutane 18 sun jikata a wani taho mu gama da aka yi tsakanin ´ya´yan Hamas da Fatah da ba sa ga maciji da juna.