An shiga kwana na biyu na fada a Nasriya | Labarai | DW | 19.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An shiga kwana na biyu na fada a Nasriya

Yan sanda a Iraki sunce an shiga kwana na biyu na bata kashi tsakanin sojojin Mahdi da jamian tsaro a Nasriya inda mutane 8 suka rasa rayukansu wasu kuma 60 suka samu raunuka yawancinsu yan sanda a jiya litinin.

Da safiyar yau din an kai hari kan hedkwatar yan sanda na birnin inda wasu yan sanda uku da wasu farar hula 2 suka samu raunuka.

Sojojin na Mahdi dai magoya bayan malamin shia ne Moqtada as Sadr.

Jamian yankin sunce wasu yan kabilun Nasriyan sun shiga cikin fadan suna marawa yan sanda baya a kokarinsu na fitar da sojojin na Mahdi daga garinsu.

Sojojin Amurka dana Iraki kusan 10,000 ne kuma suka kaddamar da hari kann yan kungiyar alQaeda da safiyar yau din nan