An sasanta a tsakanin Chad da Sudan | Labarai | DW | 09.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sasanta a tsakanin Chad da Sudan

Shugabannin kasashen chadi da Sudan sun rattaba hannu kann yarjejeniyar kawo karshen tashe tashen hankulan dake faruwa a iyakar kasashen biyu.

Shugaba Omar El Bashir na Sudan da Idiris Debby na Chad, sun cimma wannan yarjejeniyar ne a daren jiya laraba wayewar garin yau Alhamis a can birnin Tripoli na kasar Libya.

Rahotanni dai sun nunar da cewa an samu cimma wannan matakin ne, a lokacin wani dan kwarya kwaryan taron kwana daya da shugaba Mohd Ghaddafi na Libya ya dauki nauyin gudanar dashi.

Kafin dai cimma wannan yarjejeniya, kyakkyawar dangantaka dake tsakanin kasashen biyu ta fuskanci koma baya , bayan da kasashen biyu ke sukar juna da ingiza wutar rikice rikice a tsakanin juna.