An sanya hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin kawance a Jamus | Labarai | DW | 19.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sanya hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin kawance a Jamus

Bayan shawarwari na tsawon makonni 4 a jiya juma´a jam´iyun Christian Union da SPD sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa babbar gwamnatin kawance. A bikin sanya hannu an jiyo shugabar gwamnatin Jamus mai jiran gado kuma shugabar CDU Angela Merkel na cewa sabuwar gwamnatin zata sake daga matsayin Jamus. Shi kuwa a nasa bangaren shugaban SPD Matthias Platzeck cewa gwamnatin kawancen na sane da nauyin da ke kanta. Ya ce manufa ita ce ta da komadar tattalin arziki tare da kare manufofin jin dadin jama´a. A ranar talata mai zuwa majalisar dokoki ta Bundestag zata zabi Merkel a mukamin sabuwar shugabar gwamnati.