An sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar EU | Siyasa | DW | 13.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar EU

An yi bukin rattaba hannu kan yarjejeniyar a birnin Lisbon

default

Tutocin ƙasashe 27 na EU

A yau alhamis a hukumance shugabannin tarayyar Turai suka yi bukin sanya hannu kan wata yarjejeniyar yiwa ƙungiyar EU canje canje da nufin karfafa wannan ƙungiya da aka kara yawan membobin ta. An yi wannan buki ne a birnin Lisbon na ƙasar Portugal.

Kwanaki ƙalilan bayan kammala taron kolin ƙungiyar tarayyar Turai EU a cikin watan yuni, an jiyo shugabar gwamnatin Jamus kuma tsohuwar shugabar tarayyar Turai Angela Merkel na cewa.

“Mun amince akan ka´idojin wata sabuwar yarjejeniya ga kungiyar EU. Mun kawad da saikon da aka samu. A ƙarshen ba mu ba wa mara da kunya ba. Mun hana samun rarrabuwar kawuna.”

Da ƙyar da gumin goshi shugabanni 27 na ƙasashen EU suka amince da sabbin yarjeniyoyi guda biyu da aka yiwa kwaskwarima. Ɗaya na matsayin wani harsashen ƙungiyar yayin da ɗayar ta zayyana yadda kungiyar zata tafiyar da aikinta. Wannan amincewa na da muhimmanci musamman ga ƙasashen da ba su da wakilci cikin kungiyar, wato kamar na yankin Balkan da Turkiya, kamar yadda Jo Leinen shugaban kwamitin tsara kundin tsarin mulkin ya nunar a shekara ta 2006.

“Ba zamu iya faɗaɗa majalisar dokokin Turai ba idan ba a samu kundin tsarin mulki ba. Kasashen Romaniya da Bulgariya sun rigaya sun samun karɓuwa a ƙarƙashin yarjejeniyar Nice. Amma ga ƙasashe Kuratiya da Mazedonia da sauransu za a fuskanci matsala. Saboda haka ya ke da muhimmanci a samu madafa kan kundin tsarin mulkin.”

Ko da yake an yi watsi da tsarin mulkin sakamakon kuri´ar raba gardama da aka gudanar a Faransa da NL amma har yanzu yarjejeniyar ta na nan. Bambamcin da ke akwai bai da yawa, wato suna kadai aka canza. Duk wani abin da ke yin tuni da matsayin wata kasa an fitar daga cikin kundin sai kuma sunan da za a bawa jami´in kula da harkokin wajen ta.

A ƙarƙashin sabuwar yarjejeniyar kungiyar EU zata samu shugaba mai wa´adin mulki na shekaru biyu da rabi. Sai jami´in harkokin waje wanda ba za´a ba shi sunan minista ba amma aikin zai kasance irin na minista ne. Sannan a shekara ta 2014 za a rage yawan hukumar kungiyar yayin da majalisar Rurai zata samu yawan kujeru 751. Tsarin yawan rinjayen kuri´u zai maye gurbin tsohon tsarin da ake bi mai daure kai.

Yarjeniyoyin guda biyu zasu maye gurbin yarjejeniyoyi guda 8 da aka ta amincewa da su cikin shekaru 56 da suka wuce. Yanzu bayan bukin rattaba hannu kan yarjejeniyar, bisa al´ada a gobe juma´a shugabannin na EU zasu sake haɗuwa a birnin Brussels don gudanar da taron ƙoli na ƙarshen shekara.