1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sanarda ranar zabe a Rasha

Majalisar dattijan Rasha ta ce za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a ranar 2 ga watan Maris na shekara ta 2008.Wannan kuwa yana bisa tsarin dokokin tsarin mulkin kasar ne wanda ya haramtawa shugaban kasa mulki na waadi fiye da biyu.Karkashin dokokin Rasha masu tsayawa takarar shugaban kasa dole ne su mika takardun na neman tsayawa cikin kwanaki 25 bayan an tabbatar da tsayarda ranar zabe.