An samu ′yar Chibok daya | Labarai | DW | 18.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu 'yar Chibok daya

An samu daya daga cikin 'yan matan Chibok 'yan makaranta da 'yan Boko Haram suka sace fiye da shekaru biyu a Najeriya.

Rahotanni daga Najeriya na cewa an samu daya daga cikin 'yan mata 'yan makaranta na Chibok wadanda tsagerun kungiyar Boko Haram suka sace fiye da shekaru biyu da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito 'yan gwagwarmya da shugaban al'umma suna tabbatar da labarin. Fiye da shekaru biyu da suka gabata aka sace 'yan mata fiye da 200 a garin Chibok na Jihar Borno da ke yabnkin arewa maso gabashin Najeriya, inda tsagerun na Boko Haram suka yi sanadiyar mutuwar dubban mutane.