An samu tsohon mataimakin shugaban Kongo da laifi
March 21, 2016Talla
Kotun hukuntan manyan laifukan yaki ta duniya ta samu Jean-Pierre Bemba tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo da laifin ta'asa na yaki da dakarunsa na-sa-kai suka aikata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Alkalan kotun sun samu Bemba da duk laifuka biyar da aka tuhume shi wadanda mayakan sa-kai da ke karkashin ikonsa suka aiwatar a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Shi dai Jean-Pierre Bemba tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo ya zama wani babban jigo da kotun ta samu da laifi.