An samu tsaiko a tattaunawar yankin Gabas ta Tsakiya | Labarai | DW | 25.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu tsaiko a tattaunawar yankin Gabas ta Tsakiya

An samu cikas a tattaunawar zaman lafiya tsakanin Israila da Palasɗinawa bayanda Palasɗinawa sun ce ba za a samu ci gaba ba har sai Israila ta dakatar da gine ginenta a yankunan Palasɗinawa. Ma’aikatar kula da gidaje ta Israilan ta ɓullo da wani shiri na gina gidaje 500 a garin Har Homa da kuma wasu 240 a yankin Maale Adumin dake kusa da birnin Ƙudus a shekara mai zuwa. Wannan shiri dai ya janyo suka da ba a zata ba daga Amurka da kuma Ƙungiyar Taraiyar Turai. Babban mai shiga tsakani na Palasɗinawa Ahmed Qurie ya fadawa takawararsa ta Israila Tzipi Livni cewa dole ne Israila ta zaɓa tsakanin hanyar zaman lafiya da tattaunawa ko kuma hanyar ci gaba da gina gdajen share guri zauna. Firaministan Israilan Ehud Olmert da shugaban Palasɗinawa Mahmud Abbas zasu gana cikin wannan mako a ƙoƙarinsu na farfaɗo da tattaunawar da aka ƙaddamar da ita a taron da suka yi a ƙasar Amurka a watan da ya gabata.