An samu sabuwar shugabar gwamnati a Jamus | Labarai | DW | 22.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu sabuwar shugabar gwamnati a Jamus

Yan majalisar dokokin Tarayyar Jamus ,wato Bundestag sun kada kuriun amincewa da Angela Markel, a matsayin sabuwar shugabar gwamnatin Jamus.

A lokacin zaman majalisar dokokin, Angela Markel ta samu amincewar yan majalisa 397 daga cikin yan majalisu 614.

Wannan dai amincewa tazo ne watanni kadan da suka gabata, bayan tirmin danyar da aka fuskanta a sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan satumba na wannan shekara da muke ciki, duk kuwa da cewa jamiyyar CDU da CSU nada rinjayen kujeru hudu akan jamiyyar SPD.

Ya zuwa yanzu dai ,Angela Markel, wacce ta fara aiki a safiyar yau a matsayin shugabar gwamnatin Jamus, ta kasance Mace ta farko data taba kasancewa a wannan mukami a tsawon tarihin Jamus.

Angela Markel, wacce ake mata kirari a matsayin mace mai kamar maza, ta kuma kasance mutum na farko daya taba rike wannan mukami daga gabashin kasar ta Jamus.