An samu raguwar ´yan gudun hijira a duniya | Labarai | DW | 09.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu raguwar ´yan gudun hijira a duniya

Yawan ´yan gudun hijira a duniya baki daya ya ragu zuwa kasa da wani matsayi da bai taba kaiwa ba tun kimanin shekaru 26 da suka wuce. To amma a lokaci daya yawan ´yan gudun hijira a cikin kasa ya karu. Hakan dai na kunshe ne a cikin kididdiga ta shekara shekara da hukumar kula da ´yan gudun hijira ta MDD ta bayar. Alkalumman da hukumar ta bayar sun nunar da cewa yawan ´yan gudun hijira dake tserewa yake yake a cikin gida zuwa ketare ya ragu daga mutum miliyan 9.5 zuwa milin 8.4. Amma yawan mutanen dake zaman gudun hijira a cikin kasashensu na asali ya karu ya zuwa mutum miliyan 6.5. Daukacin ´yan gudun hijirar kuwa sun fito ne daga kasashen Afghanistan, Kolumbia da kuma Iraqi. Sannan ´yan gudun hijira na cikin gida kuma sun fi yawa a Kolumbia da Iraqi.