An samu raguwar mace mace da kyanda ke haddasawa | Labarai | DW | 19.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu raguwar mace mace da kyanda ke haddasawa

Hukumomin kula da lafiya sun sanarda raguwar kashi sittin cikin dari na mace machen yara sakamakon cutar kyanda,wanda suka danganta da taimakon euro miliyan 5 domin rigafi da akayi.

Kungiyoyi dake da lahakin gudanar da yekuwar kawadda cutar sunce an samu raguwar wadanda suke mutuwa sakamakon cutar daga mutum 873,000 a 1999 zuwa mutum 345,000 a 2005 a cikin duniya baki daya.

An samu raguwar yawan wadanda suke rasa rayukansu sakamakon cutar ce,musamman saboda yadda cutar tayi kasa a nahiyar Afrika.

Darekta janar ta hukumar lafiya ta duniya Dr.Margaret Chan ta baiyana wannan sakamako da cewa nasara ce babba ga fannin kula da lafiya a duniya.