An samu raguwar kwadagon tilas ga kananan yara | Labarai | DW | 04.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu raguwar kwadagon tilas ga kananan yara

Wani rahoto da kungiyar kwadago ta duniya wato ILO ta bayar ya nuni da cewa daga shekara ta 2000 zuwa ta 2004 an samu raguwar yawan yaran da ake tilasta musu yin kwadago a fadin duniya baki daya. Kungiyar ta ce a cikin shekara ta 2004 kananan yara maza da mata kimanin miliyan 218 abin da yayi kasa da kimanin kashi 11 cikin 100 idan aka kwatanta da yawansu a shekaru 4 da suka gabata na yaran da ke aiki don samun kudaden duba kansu. An fi samun ci-gaba a kasashen Latun Amirka da Karibean. A nahiyar Asiya ma yawan yaran da ke aikin dole ya ragu ainun. To amma har yanzu akwai kananan yara kimanin miliyan 122 dake kwadagon tilas a kasashen na Asiya. A kasashen Afirka kuwa musamman na yankin kudu da Sahara daya bisa 4 na yara ne ke aiki don samarwa kansu da kuma danginsu abinci.