An samu ragowar kwararar bakin haure zuwa Turai | Labarai | DW | 15.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu ragowar kwararar bakin haure zuwa Turai

Kungiyar EU ta ce adadin bakin haure da ke ketarawa ta kasashen Nijar da Libiya zuwa Turai ya ja baya da kashi dari bisa dari tsakanin watannin Mayu da Nowambar 2016.

Kungiyar Tarayyar Turai ta jinjina wa kasar Nijar da wasu kasashen Afirka bakar fata dangane da rawar da suke takawa wajen hana kwarara bakin haure da suke bi ta kasashensu zuwa Turai. Kungiyar ta EU ta bayyana a jiya Laraba cewa adadin 'yan kasahen Afirka bakar fata da ke ratsawa ta kasar Nijar zuwa kasar libiya domin ketarawa cikin Turai ya ragu da kashi dari bisa dari tsakanin inda yawan masu ketarawar ya sabko daga mutun dubu 70 a watan Mayu zuwa dubu daya da 500 kawai a watan Nowambar. 

Kasashen Afirka biyar ne dai da suka hada da Senegal da Mali da Najeriya da Habasha da Nijar Kungiyar ta EU ta cimma yarjejeniyar taimaka masu da kudi domin su bada hadin kansu ga matakin EU na hana kwararar bakin haure da ke kasadar ratsa ruwan Tekun Mediterraneen zuwa kasashen Turan. Matakin da wasu Kungiyoyin masu fafutika suka yi tir da Allah wadai da shi a bisa hujjar cewa ya saba wa ka'ida.