An samu ma′aikata bogi 17000 a Najeriya | Labarai | DW | 20.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu ma'aikata bogi 17000 a Najeriya

Hukumar yaƙi da masu yiwa arzikin kasa ta'ananti a Najeriya watau EFCC ta ce an samu mai'aikatan na bogi waɗanda yawansu ya kai dubu 17 wanda gwamnatin take biya albashi, ba tare da sun yi aikin ba.

A wani taron manema labarai da ya kira shugaban hukmar ta EFCC Ibrahim Magu ya ce kawo yanzu addadin mai'katan na bogi ya kai sama da dubu 37.

A cikin watannin biyun da suka gabata gwamnatin Najeriyar ta gano ma'aikatan na jabu har kusan dubu 20 waɗanda gwamnatin ta riƙa zubawa kuɗaɗen albashi Naira biliyan ɗaya. Ibrahim Magu wanda ya ce hukumar ta ƙaddamar da wannan aikin bincike ne tare da ofishin ministan kuɗi ya yi gargadin cewar mai yi wa addadin ya ƙaru a ci gaba da aikin binciken da ake yi