1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu karuwar haihuwar jarirai a Jamus

Gazali Abdou Tasawa
March 28, 2018

Wasu alkalumman bincike na hukumar kididdiga ta kasar Jamus da aka wallafa a wannan Laraba sun nunar da cewa a shekara ta 2016 an samu karuwar haihuwa wadda ba a taba samun kamarta ba tun a shekarar 1973.

https://p.dw.com/p/2v9jg
Symbolbild Mutter
Hoto: imago/imagebroker

Alkalumman wadanda ma'aikatar kididdiga ta kasar ta Jamus ta wallafa a wannan Laraba sun nunar da cewa an samu karuwar haihuwa da kashi bakwai cikin dari a shekarar 2016 inda a jumlace aka haifi jarirrai kimanin dubu 792. 

Sai dai hukumar ta ce lamarin na da nasaba ne da karuwar mata 'yan asalin kasashen waje da aka samu a kasar ta Jamus a sakamakon kwararar 'yan gudun hijira.

Alkalumman dai sun nunar da cewa matan Jamusawan sun haifi jarirrai dubu 607 da 500, a shekarar ta 2016 a yayin da mata 'yan asalin kasashen waje suka haifi jarirrai dubu 184 da 660. 'Yan gudun hijira kimanin miliyan daya ne dai akasarinsu daga kasashen Siriya da Iraki da Afganistan, Jamus ta karba a shekara ta 2015 kadai.