1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

An samu karuwar cutar tarin fuka a duniya

Gazali Abdou Tasawa
October 13, 2016

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin cewa barnar da annobar tarin fuka ke yi ta wuce kimar duk yadda ake tunani, inda ko a shekarar da ta gabata mutane miliyan 10 da dubu 400 suka kamu da wannan cuta.

https://p.dw.com/p/2RCeL
Tuberkolose
Hoto: picture-alliance/dpa

 

Kungiyar ta WHO ta sanar da hakan ne a cikin wani rahoto da ta fitar a wannan Alhamis inda ta ce tana fuskantar kalubale wajen tattara kudade na gudanar da binciken samar da allura ko kuma wasu magunguna na warkar da cutar. 

Babbar darakta hukumar Margaret Chan ta ce doli sai kasashen duniya sun kara hobbasa idan ana so a kawo karshen barazanar da wannan annoba mai kisa ke yi wa al'ummomi a kasashen duniya. 

Ta kara da cewa burin da hukumar ta WHO ke son cimma a nan gaba shi ne na rage yawan mutanen da ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar da kashi 90 daga cikin dari dama masu harbuwa da ita da kashi 80 daga cikin dari nan zuwa shekara ta 2030. 

Mutane miliyan daya da dubu dari takwas ne dai cutar ta tarin fuka ta halaka a shekara ta 2015 wanda ke nufin cewa an samu karin mutane dubu 300 ga na shekarar ta 2014.