An samu karancin allurar riga-kafin cutar sankarau a Najeriya | Labarai | DW | 30.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu karancin allurar riga-kafin cutar sankarau a Najeriya

Sama da mutane 280 cutar sankarau ta yi ajalinsu tun sake barkewarta a Najeriya a cikin watan Nuwamban bara.Jihohin Arewa maso Yammacin kasar suka fi fama da ita.

Najeriya na fuskantar karancin allurar riga-kafin cutar sankarau da ta yi sanadiyyar rayukan akalla mutane 280 tun barkewarta a cikin watan Nuwamban 2016, inji manyan jami'an kiwon lafiyar kasar. Shugaban cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya, Chikwe Ihekweazu ya ce kawo yanzu sun yi rajistar mutane kusan 2000 a fadin kasar da ake zaton sun kamu da cutar amma 109 kawai aka tabbatar, tun bayan rahoton farko a jihar Zamfara.

Jihohin Zamfara da Sakkwato da Katsina da Kebbi da kuma Neja su ne suka fi fama da cutar a wannan karon. Wani jami'in cibiyar ya bayyana karancin allurar da cewa babban lamari ne.