1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu gagarumin ci-gaba a shawarwarin kafa gwamnatin hadaka a Falasdinu

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya ce ya na sa ran kafa wata sabuwar gwamnatin hadin kan kasa nan da karshen wannan wata da muke ciki da fatan haka zai kawo karshen takunkuman hana ba da tallafi ga hukumar mulkin Falasdinawa. Abbas ya ce sun samu ci-gaba a kokarin da suke yi na kafa gwamnatin hadin kan kasa wadda zata karya kawanyar da aka yi musu kana kuma ta bude hanyar yin sulhu mai dorewa wanda zai kawo karshen mamayar har abada. Da yardar Allah za´a kafa wannan gwamnati a karshen wannan wata, inji Abbas a jawabin da yayiwa dubban Falasdinawa da suka hallara don yin juyayi na cika shekaru biyu da rasuwar magabacinsa Yasser Arafat.