An samu cigaba wajen yaƙi da cutar zazzaɓin cizon Sauro a Afirka
April 23, 2010Hukumar kula da lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewar ƙasashen Afirka na samun gagarumar ci gaba ta fuskar yaƙi da cutar zazzaɓin cizon sauro ko Malaria, wadda ke yin sanadiyyar mutuwar kimanin mutane miliyan ɗaya - a duk shekara, tare da janyo cikas ga bunƙasar tattalin arziƙinta. Darektan shirin yaƙi da Malaria a duniya a ƙarƙashin hukumar lafiyar, Rob Newman, wanda ya sanar da hakan, ya danganta ci gaban da aka samun ne da yawan rarraba gidajen sauro, da magungunan da ake yi, game da sauƙaƙa kudaɗen jinyar masu fama da cutar, inda ya bada misali da ƙasar Zambiya, wadda ta yi nasarar kawar da kusan rabin masu fama da zazzaɓin malaria daga shekara ta 2001 zuwa 2008. Ya ce, kwatankwacin nasarar da Zambiya ta samu ne ake da ita a ƙasashe - kamar Nijeriya da Jamhuriyyar Dimoƙraɗiyyar Kongo. Newman ya ƙara da cewar, hatta shi kansa yana mamakin irin ja da bayan da matsalar cutar ta yi duk kuwa da tsawon shekarun daya shafe yana wannan aiki.
Mawallafi: Babangida Jibril Edita: Yahouza Sadissou Madobi