An samu akwatunan rediyon jirgin Russia da yayi hatsari | Labarai | DW | 23.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu akwatunan rediyon jirgin Russia da yayi hatsari

Masu bincike a game da hatsarin jirgin fasinjan nan na kasar Russia daya halaka mutane 170 a jiya talata, sun samu bakaken akwatunan jirgin guda biyu.

Ana dai sa ran cewa wadannan akwatunan rediyo zasu taimaka wajen gano dalilan daya haifar da wannan hatsari, to amma ya zuwa yanzu ana danganta hatsarin ne da rashin kyawun yanayi.

Idan dai za´a iya tunawa jirgin mallakar kamfanin Pulkavo yayi hatsarin ne a gabashin kasar Ukraine ne akan hanyar sa ta zuwa St. Petersburg.

Wannan nan hatsari dai ya kasance irin sa na uku mafi muni da kasar ta Russia ta fuskanta a cikin wannan shekara