An sami ragowar maneman mafaka a nan Jamus. | Labarai | DW | 11.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sami ragowar maneman mafaka a nan Jamus.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta nan Jamus, ta buga wasu alƙaluma, waɗanda ke nuna cewa, yawan maneman mafaka a nan ƙasar na ci gaba da raguwa. A cikin wata sanarwar da ta bayar yau a birnin Berlin, ma’aikatar ta ce tsakanin watanni Janairu zuwa Nuwamba na wannan shekarar, mutane dubu 20 ne suka nemi mafaka a nan ƙasar. Hakan kuwa ya kasance ragowar kashi 27 cikin ɗari ke nan, idan aka kwatanta wannan adadin da na alƙaluman bara. Mafi yawan maneman mafakan kuma, sun fito ne daga Iraqi, da Serbiya da kuma Turkiyya, inji sanarwar.