An sami fashewar bututunan mai a kafofin haƙo man fetur a tarayyar Najeriya. | Labarai | DW | 13.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sami fashewar bututunan mai a kafofin haƙo man fetur a tarayyar Najeriya.

Bakin haure daga Senegal

Bakin haure daga Senegal

A tarayyar Najeriya, an sami tagwayen fashewar bututun mai a wasu kafofin haƙo man fetur na kamfanin Agip da ke yankin Naija-Delta. Jami’an gwamnati sun ce suna tuhumar ’yan ɓata gari ne da janyo fashewar bututun a jihar Bayelsa. Har ila yau dai, babu wanda ya yi ikrarin kai hari a kan kafofin.

Tun farkon wannan shekarar dai, hare-haren da ’yan ta kife suka yi ta kaiwa a kan kafofin hakon man fetur, a yankin na Naija-Delta, ya janyo asarar kusan kashi 20 cikin ɗari, na yawan man garwa miliyan biyu da rabin da Najeriya ke fitarwa a ko wace rana zuwa ƙetare. Wannan rikicin dai, ya janyo hauhawar farashin man fetur a kasuwannin duniya.