1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sami ƙarin yawan baƙin haure a kan tsibirin Canary.

Jami’an tsaro a kan tsibirin nan na Canaries da ke ƙarƙashin ikon Spain, sun ce sun kame ƙananan kwale-kwale da ke ɗauke da baƙin haure ɗari 2 da 50 daga nahiyar Afirka, a cikin sa’o’i 24 da suka wuce. Tun farkon wannan shekarar dai, fiye da baƙin haure dubu 10 ne suka sauka a kan tsibirin. Ministan harkokin wajen Spain, Miguel Angel Moratinos, ya gana da takwarorinsa na Afirka a ran talatar da ta wuce, don tattauna hanyoyin shawo kan wannan matsalar. A wata mai zuwa ne dai, za a gudanad da wani taro na ƙasa da ƙasa a birnin Rabat na ƙasar Maroko, don tattauna wannan batun.