1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sallami wakilan Hamas daga gwamnatin hadaka

Shugaban yankin Palasdinawa Mahmud Abbas, ya katse dangantar dake tsakanin gwamnatin sa da kungiyyar masu tsatsauran ra´ayi ta Hamas.Al´amarin ya faru ne bayan da shugaban ya sallami duk wani dan kungiyyar, dake rike da wani babban mukami a cikin gwamnatin ta Palasdinu .Tuni dai kungiyyar ta Hamas ta mayar da martanin hawa kujerar naki a game da wannan mataki.Kafin dai daukar wannan mataki, kungiyyar ta Hamas nada mukamai kusan dari biyu a cikin gwamnatin hadakar, da shugaba Abbas kewa jagoranci.