1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sallami wakilai 4 daga gwamnatin rikon kwayar Somalia

June 5, 2006
https://p.dw.com/p/BuvM
Somalia ta sallami madugan yaki 4 dake rike da mukamai a cikin gwamnatin rikon kwarya bayan ta same su da hannu a fadace fadacen da ake gwazbawa a babban birnin kasar Mogadishu. Wani kakakin gwamnati ya ce an dauki wannan mataki a wani taro na musamman da majalisar ministoci ta yi a birnin Baiduwa, inda gwamnatin rikon ta kafa sansani. ´Ya´yan majalisar dokoki kuma sun bukaci da a caji mutane da aikata laifin yaki. Dukkan mutanen hudu dai na membobin kawancen nan ne na madugan yaki, wadanda ake zargin cewa gwamnatin Washington na marawa baya. Artabun da ya barke a birnin Mogadishu cikin watan fabrairu tsakanin sojojin sa kai na kungiyoyin Islama da kuma mayakan kawance haulolin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 350 daukacin su fararen hula.