1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sallami turawan da a ka kama kussa da iyakar Niger da Tchad

August 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bult

Sabbin rahotani daga opishin ministan harakokin wajen ƙasar Italia, sun ce an sallami,turawan nan, yan yawan shaƙatawa, da a ka yi awan gaba da su, a gabacin Jamhuriya Niger, kussa da iyaka da ƙasar Tchad.

Kakakin ministan ya ce, baki ɗayan su, an sako su, kuma su na cikin ƙoshin lahia.

Bisa dukan alamu, a cewar sa, wanda su ka aikata kamun, sun yi hakan ne kawai, da nufin lalube yan kuɗaɗen turawan.