An sallami turawa 6 da a ka yi garkuwa da su a yankin Niger Delta | Labarai | DW | 24.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sallami turawa 6 da a ka yi garkuwa da su a yankin Niger Delta

Rahotani daga Taraya Nigeria, sun ce matasan yankin Niger Delta, sun yi belin turawan nan 6, da su ka yi garkuwa da su, bayan kwanaki 10 su na cikin hannun su.

An sace wannan turawa, masu aiki a kampanonin haƙo man petur, ranar 13 ga watan da mu ke ciki, a wani gidan rawa na Port harcurt.

Sun haɗa da Ingillawa 2 ,da ba´amurike ɗaya, da bajamishe ɗaya, sannan 1 na Irland, da kuma guda dan ƙasar Poland.

Kakakin gwamnatin Jihar Rivers, Magnus Abe, ya ce su na cikin alamun ƙoshin lahia.

Ya zuwa yanzu, mutum ɗaya tilo, ya rage a cikin hannun matasa daga jimillar baƙi 17, da su ka kame a cikin wannan wata.