An sallami hafsan hafsoshin sojan Jamus daga muƙaminsa | Siyasa | DW | 26.11.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An sallami hafsan hafsoshin sojan Jamus daga muƙaminsa

A sakamakon taɓargazar wani harin da aka kai kan dakarun ƙungiyar Taliban, wanda ya rutsa da farar hula watan satumban da ya wuce, an sallami hafsan hafsoshin sojan Jamus daga muƙaminsa

default

Hafsan hafsoshin sojan Jamus Wolfgang Schneiderhan

Shi dai hafsan hafshin sojan na Jamus, Wolfgang Schneiderhan, wanda kamar yadda ministan tsaro Karl-Theodor zu Guttenberg ya nunar, shi kansa ne ya ƙaddamar da takardar murabus daga muƙaminsa yau alhamis, ana zarginsa ne da rowar wasu bayanai akan harin ta jiragen saman yaƙin ƙungiyar tsaro ta NATO ranar 4 ga watan satumban da ya gabata. Sallamarsa daga kan muƙamin dai ta biyo bayan wani rahoto ne da jaridar Bildzeitung ta rubuta yau alhamis ɗinnan dake fallasa taɓargazar kisan farar hula a matakin na kai farmaki kan dakarun Taliban. An saurara daga bakin ministan tsaro Karl-Theodor zu Guttenberg yana mai faɗi cewar:

"Ina dai so in bayyana ra'ayina a game da rahoton asiri da jaridar Bildzeitung tayi batu kansa a yau. A haƙiƙa ba ni da wata masaniya a game da wannan batu lokacin da na yi bayani akan rahoton kwamandan rundunar ISAF, wanda na gabatar a karon farko a jiya. Wannan bayanin da sauran bayanai dake da tushe daga gwamnatin da ta gabata ba a gabatar da su ba. A wannan ɓangaren an ɗauki matakan da suka dace kan masu alhakin lamarin, inda hafsan hafsoshin soja ya nema daga gare ni da in sallame shi daga muƙaminsa, kazalika shi ma ƙaramin minista a ma'aikatar tsaro Wichert, shi ma ya amince da alhakin dake kansa."

Bundesverteidigungsminister Karl-Theodor zu Guttenberg CSU

Ministan tsaro Karl-Theodor zu Guttenberg

Rahoton na jaridar Bildzeitung dai yayi nuni ne da cewar akwai wasu cikakken bayanai da aka tara a bincike na farko da aka gudanar akan harin, wanda kuma ke nunarwa a fili cewar matakin ya rutsa da farar hula. A wancan lokaci, kamar yadda jaridar ta nunar, shelkwatar sojojin na Jamus dake Mazari-Sharif ta gabatar da cikakkun bayanai zuwa ma'aikatar tsaro dake Potsdam inda tayi batu game da farar hula da suka haɗa wasu yara matasa su biyu. Amma ba a gabatar da waɗannan bayanan ga lauya mai ɗaukaka ƙara da sunan gwamnati ba. Shugabar gwamnati Angela Merkel dai ita ce ta farko da ta fito ta nuna cewar gwamnatin Jamus zata yi matuƙar baƙin ciki in har harin ya rutsa da farar hula kwanaki kaɗan bayan afkuwarsa. To sai dai kuma a baya ga waɗannan bayanai, akwai kuma wasu finafinai na bidiyo da ɗaya daga cikin sojan Amirka dake da hannu a harin ya ɗauka, wanda ke nuna yadda aka ɗauki matakin a cikin garaji ba tare da neman cikakken bayani ba. A dai halin da ake ciki yanzu tsofon ministan tsaron Jamus Franz-Josef Jung ya ce nan in an jima zai tofa albarkacin bakinsa akan wannan zargi.

"Ina fata za a ba ni wata dama ta binciken waɗannan bayanai da aka gabatar da yanayin da aka kasance a ciki ta yadda zan samu cikakkiyar bayyana ra'ayina gaban majalisar dokoki. Ina fatan hakan zai samu a yau ɗin nan."

Franz-Josef Jung in Afghanistan

Tsofon ministan tsaron Jamus Franz-Josef Jung

A zaman taron da majalisar dokokin ke gudanarwa dai, maganar ƙara wa'adin aikin sojojin na Jamus a Afghanistan ita ce ta mamaye zauren majalisar.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu