An sako Turawan nan uku da aka tsaresu a Kenya | Labarai | DW | 19.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sako Turawan nan uku da aka tsaresu a Kenya

Rahotanni daga Kenya sun ce an saki Bajamushen mawaƙin jazz da aka kama ranar alhamis Andrej Hermlin. Hakazalika rahotannin sun shaidar da cewa an sako sauran Turawa biyu wato Bajamushe ɗaya da wata ´yar Holland waɗanda aka kama bisa zargin aikata ta´addanci a Kenya. Shi dai Hermlin abokin jagoran ´yan adawan Kenya ne wato Raila Odinga. Mutanen sun je kasar nan don shirya wani fim kan tarihin dan adawan na ƙasar, amma aka kama su bisa zargin yin wasu abubuwa da suka karya dokar ƙasa.