An sako tsohon shugaban Rwanda daga kurkuku | Labarai | DW | 06.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sako tsohon shugaban Rwanda daga kurkuku

A kasar Rwanda an sako tsohon shugaban kasar Pasteur Bizimungu daga gidan fursuna bayan ahuwa daya samu daga shugaban kasar mai ci yanzu kann hukuncin daurin shekaru 15 da akayi masa bisa zargin haddasa rikicin kabilanci a kasar.

Pasteur Biszimungu wanda yayi murabu s a 2000,an daure shine tun 2004 cikin wata sharia da masu suka suka ce akwai siyasa a ciki.

Ana dai zarginsa ne da laifukan kirkiro da rundunar sojin sa kai da yin sama da fadi da kudaden gwamnati tare da haddasa fitina tsakanin kabilun kasar.