An sako maaikatan shell da akayi garkuwa da su a Najeiya | Labarai | DW | 12.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sako maaikatan shell da akayi garkuwa da su a Najeiya

A Najeriya an sako dukkanin wadanda akayi garkuwa da su 60 a yankin Naija Delta.

A ranar talata ne dai matasa dauke da bindigogi suka kame gidan mai na shell a jihar bayelsa.

Kanfanin na shell ya bada rahoton cewa,jamaar kauyukan da suka kame wadannan mutane suna kokawa ne da rashin kula da jin dadin rayuwarsu.

Fada tsakanin kanfanonin mai da alummomin dake yankin dake neman a basu aikin yi saboda filayensu da ake anfani da su ana hako kusan mafi yawa na ganga miliyan 2 da rabi da a kullum a taraiyar ta najeriya.

Tashe tashen hankulam na naija delta talauci da rashin bin doka da oda ke kara ingiza su.

Yanzu haka kuma har yanzu akwi wasu maaikatn mai turawa 7 da suka bace a tashe tashen hankula makon daya gabata.