1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sako ma’aikatan kamfanin Agip da aka yi garkuwa da su a Najeriya.

Rahotanni daga tarayyar Najeriya sun ce an cim ma sako wasu ma’aikatan kamfanin haƙo man fetur nan Agip, su 16 da sojoji 8 da ke kare lafiyarsu, waɗanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da su tun ran talatar da ta wuce. Hakan kuwa ya samu ne bayan da gwamnatin ƙasar ta biya ɗimbin yawan kuɗaɗen diyya ga ’yan bindigan, inji rahotannin. A yankin na Niger Delta da ke kudancin Najeriyan dai, an sha yin garkuwa da ma’aikatan haƙo man fetur, inda masu yin garkuwan ke bukatar a biya su maƙudan kuɗaɗe, kafin su sako waɗanda suka kamen. Sai dai har ila yau mahukuntan Najeriyan na ƙaryata cewa, suna biyan ’yan tawayen diyya.