An sako maaikacin BBC da akayi garkuwa da shi Gaza | Labarai | DW | 04.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sako maaikacin BBC da akayi garkuwa da shi Gaza

An dan jaridar nan maaikacin BBC Alan Johnston wanda yan takife sukayi garkuwa da shi a zirin Gaza a ranar 12 ga watan Maris.

Rahotanni sunce yana cikin koshin lafiya.Johnston ya baiyanawa manema labari farin cikinsa ganin an sako shi ya kuma baiyana irin fargaba da ya shiga a hannun wadanda suka sace shi.

Kungiyar Hamas ce dai tayi kokarin ganin an sako Johnston tana mai baiyana cewa hakan zai maido da martabar Palasdinawa.

Hambararren firaminista Ismail Haniya bayan karbo johnston din ya kuma baiyana fatar cewa zaa cimma wata yarjejeniya ta sako sojan nan na Israila Gilad Shalit da akayi garkuwa da shi a Gaza tun watan yuni na shekarar data gabata.