An sako Jamsuwan da ak yi garkuwa da su a Yemen | Labarai | DW | 31.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sako Jamsuwan da ak yi garkuwa da su a Yemen

Masu garkuwa a kasar Yemen sun saki tsohon babban jami´in diplomasiyar Jamus Jürgen Chrobog da sauran iyalinsa. Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya tabbatar da haka a birnin Berlin. Ministan ya ce Chrobog da matarsa da kuma ´ya´yan sa 3 na hannun hukumomin Yemen kuma yanzu haka an kai su birnin Aden. A ranar labara da ta wuce wasu ´yan kabila suka sace Jamusawan a lokacin da suke yawon bude ido a yankin Shabwa dake gabashin Yemen. Kamfanin dillancin labarun Yemen ya rawaito cewar an kame masu garkuwa su hudu. Sannan an saki direbobi 3 ´yan Yemen wadanda su ma aka yi garkuwa da su tare da Jamusawan.